Cigaba Inganta Harshen Mboyawa

A cikin tafiyan da ake ciki na ci gaban al'ummar Mboi, an fara ne da Hon. Javan Jambali, wanda yayi namijin kokari wajen rubuce-rubuce game da harkar yare da dangantakarta da al'adu na wannan al'ummar, sai kuma Dr. Jenifer Joshua wanda tayi takaitacen rubutu game da bambancin harshe da ake samuwa a sakanin yaren.

Daga nan sai Dr. Roger Blench (PhD) wanda yake da marmari da yekinin rubuce-rubuce game da yarurukan Afrika, yana mai yarda da Dr. Jenifer bisa ga bayanenta na al'ummar Mboi.

Yanzu haka, Abi Benson Silon ne wanda yake da zagewa da niyya akan kabilarsa, ta hakan ne yake da hazaka a kan al'ummar Ɓəna-Yungur, ya zo ne da cikaken hazaka ba domin rubutun waɗannan ababen da aka ambata a bisa kaɗai ba amma domin ci gaban kasar Ɓəna-Yungur, Mboi da kuma waɗansu yarurukan Afrika. Domin wannan ne ya soma bada hankali akan yaren Mboi domin ya yi rubuce-rubuce na harkar yare da dangantakarta da al'adu.

Biye wa wannan kwazon nasa akan kaɗan daga cikin masu yawan da ya gano, tuni ya rubuta Kamus na yaren Mboi, kuma ya kirkiri yanar gizo domin wannan al'ummar saboda su iya yi da kalubalan wannan zamani da zasu iya yin barazanar ɓacewa ko mutuwar wannan kabila.

Abi Benson yana da ababe masu yawa da zai faɗa game da alamuran yau da kullum game da al'ummar Mboi da cewa su yi begen samuwa idan akwai goyon bayan 'ya'yanta maza da mata.

1. Kamus na yaren Mboi (wanda aka rubuta da wallafaffe duka).

2. Taswirar gaɓoɓin jikin mutum (Gaɓoɓin jikin mutum). Parts of a Human Body.pdf

3. Harufan Mboi (Harufa da kuma ka'idodin rubutu na yaren Mboi). Kawoyi ɗa ihyã Mboi.pdf da kuma The Grammar of Mboi Language.pdf

4. Initiating Programmes to foster language use in her land such as: Bible Translation

GənaRike ɗa ni Lukawa Handa.pdf (Bishara daga hannun Luka) a harshen Handa

GənaRike ɗa ni Lukawa.pdf (Bishara daga hannun Luka) a harshen Mboi

, Binciken Littafi Mai Tsarki, Addu'ar Ubangiji, Shaidar Bangaskiya ta Masu bi. d.s..