Tarihin Mutanen Mei-Mboi a Nijeriya

Mutanen Mei-Mboi sun samu asali ne daga Hasumiyar Babila, a inda tarihin Baibul ta zayyana cewa wurin ne ya zama farkon wuri na samun ire-iren yaruruka da kuma mabambantansu. Gungun mutane na farko da suka gano junan su a sakamakon yin amfani da "ɓoi, mei" wanda take nufin 'ɗan uwa, na ce ba'. Game da yawan yin amfani da waɗannan ga kunnen sauran yaruruka, sai sauran yarurukan sun gane su da mutanen ɓoi ko Mei, shi ya sa kake ji ana kiransu "mutanen Mboi" (ɓoi). Amma kuma suna kiran kansu Mei. Mutanen nan suna da zama a cikin Karamar Hukumar song a Jihar Adamawa na Jam'uriyar Nijeriya da ke gaɓar Yammacin Afika. Mutanen Mboi na da ɗimbin tarihi mai gagarumar wadatarwa wanda sun haɗa da wuraren asali, wuraren yaɗa zango, sai zamansu da makwabtansu. waɗannan mutane dai sun fi sa hankali ne akan noma, kira, farauta, da kuma kiwo. Ba-Mboye na asali yana ɗauke da son raye-raye masu sa nishaɗi da kuma girmama addininsa na gargajiya har zuwa lokacin da Misionari sun kawo addinin kirista a yankinsu.  Mutanen Mboi na da alaka mai karfi kabilun yungur, Lala, Bata, da Ga'anda, da kuma fulanin daji masu yawoce-yawocen kiwo.

Domin karin bayyani, tuntuɓi marubucin a adreshinsa na yanar gizoː