Labaru

Al'umar Mei-Mboi tayi tashin gwauron zabbi zuwa ci gaba wurin adana tarihi wanda sun haɗa da asalinsu, wuraren da suka yaɗa zango bisa ga adanawan tarihi game da zuriyoyi, wurare masu ɗauke da ababe masu jan hankali da kuma ban mamaki kwarai. Yana kuma da zaiyananen rubuce-rubuce da ta kunshi karantace da rubutacen yare waɗanda sun taɓa manyan harsuna da bambancin su, hatta ma Kamus da kuma ababe dayawa.

Yadda Sarautar Mboi ke kan tafiya

Al'ummar Mboi ta samu Masarautar ta a madadin Mboi District a shekara ta 1992 an kuma tabbatar mata da Hakimin (Sarki) na farko Mallam Isa Aliyu Falama a wancan shekara. Sai aka rantsar da shi ranar 5/12/1993 wanda ta hakan ne yayi mulki daga watan Satumba na shekara ta 1993 zuwa ranar 12 ga wata a shekara ta 2005 ya rasu sai aka baiwa magajin sa Laminu Isa Falama daga ranar 13 ga watan Satumba 2005, ya soma tabbataciyar aiki a shekara ta 2006 zuwa ranar 3 ga watan Oktoba a shekara ta 2021.

bayan mutuwar shi Laminu, aka sa Alhaji Aminu Gudu a masayin Hakimi na hucin gadi wanda har ila yau shi Maijimilan Gudu ne yana jiran ranar da za'a ɗora wanda sarauta ta kama shi. Duk waɗannan Hakimai da aka lisafta, babu asalin BaMboye ko guda a sakaninsu, illa iyaka Fulani da Bagude (watau daga shekara ta 1992-2021).

Mazamnar kasar Mboi na kokawa da cewa Masarautar Adamawa bata yi mata adalci ba. Yaya za'a yi ana kiran sunan District da sunan kabilarsu amma kuma bare ne ke mulki? Babu adalci ko kaɗanǃ

abenson@tcnn.edu.ng ko tura sako zuwa +2347082815338   

Your encouragement is valuable to us

Your stories help make websites like this possible.